Ganduje ya turawa Sarki Sunusi takardar tuhuma kafin a dakatar da shi

Gwamnatin Jihar Kano ta aike da takardar tuhuma Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II game da tuhumar kashe kudaden masarautar Kano ba bisa ka’ida ba, kamar yadda wasu majiyoyin sirri suka tabbatar.

Dabo FM ta tattaro bayanai daga majiyoyin sirri, ciki harda mutanen fadar Sarkin Kano ta bangaren gwamnatin jihar, hadi da wasu futattun manema labarai.

Jaridar Prime Times ta rawaito cewa babban dalilin da gwamnatin jihar ta aikewa Sarkin Kano, takardar tuhumar shine domin ya samu damar kare kanshi kafin gwamnatin ta kai ga matakin dakatar dashi daga karagar mulkin Kano.

Amintattun majiyoyin sun tabbatar da aike takardar daga gwamnatin jihar Kano zuwa Sarki Kano, Muhammadu SUnusi II.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce tana ganin kamatuwar a dakatar da Sarkin Kano bisa kashe sama da Naira Biliyan 3 bata ka’ida ba.

Majiyoyi sun tabbattar da gwamnatin Kano ta karbi bayanan da hukumar yaki da cin hancin ta bayar akan dakatar da Sarki Muhammadu Sunusi II.

Dabo FM ta hada bayanan da suka tabbatar da Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu SUnsi II ya karbi takardar, kuma ana sa ran zan fito kare kanshi nan bada dadewa ba.

Sai dai daga wani bangaren, majiyoyin sunyi nuni da cewa gwamnatin jihar Kano,karkashin jagorancin gwamnan Dr Ganduje ta shirya dakatar da Sarki Sunusi a yau Alhamis,6/6/2019.

Yanzunan: Takardar da sakataren gwamnatin ya sikewa Sarki Muhammadu Sunusi II

Rahotan Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano

Hukumar karfe korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano tayi kira ga zuwa dakatar da Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, biyo bayan bannatar kudade tare da cewa ba’a kashe kudaden bisa ka’ida ba, wadanda suka kai Naira Biliyan 3.4

%d bloggers like this: