Labarai

Gwamnatin Najeriya ta siyo sabbin jiragen yaki domin kawo karshen masu garkuwa da mutane

Shugaban sojojin sama, Sadique Abubakar ya bayyana Gwamnatin Najeriya ta sayo sabbin jirage masu saukar ungulu na yaki domin fatattakar yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da Boko Harama fadin Najeriya.

Dabo FM ta rawaito Shugaban sojan saman ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a garin Abuja bayan ya gama ganawa da masu ruwa da tsaki na bangaren tsaro.

Ya kara da cewa “Akwai kayayyakin yaki da muke sa ran isowar su zuwan karshen watan Fabureru, tini jirage madu saukar ungulu na yaki sun isa tin ranar 15 ga watan Junairu.”

Kwanakin nan dai hare haren masu garkuwa da mutane, yan bindiga, Boko Haram da ISWAP sun addabi arewacin Najeriya, sai dai kuma ana fatan wannan hobbasa da jamian tsaro keyi ta kawo karshen wannan harehare da satar mutane data addabi alummar Najeriya.

Karin Labarai

UA-131299779-2