//

Agwaluma na rage karfin maza -Binciken Masana daga Jami’ar Madonna

0

Masu bincike kan magunguna sun tabbatar da cewa ‘African Star Apple’ wadda a yaren hausa aka fi sani da Agwaluma tana dakushe karfin maza.

Rahoton Dabo FM ya bayyana cewa sabon binciken ya nuna mafi yawan mutane na amfani da Agwaluma da kuma rassan ta domin magance cututtaka da dama wanda suka hada da ciwon suga, daji da cututtukan zuciya.

Rahoton jaridar Features yace binciken an samo shi ne daga ‘Faculty of Basic Medical Sciences, Madonna University,’ jihar River s. Bayan lahanta karfin maza, Agwaluma na da amfani wajen magance masassara da zazzabin cizan sauro.

Haka kuma ganyen ta na magance rudewar ciki da atini, kwallayen ta kuma na magance cututtukan mata.

Masu Alaƙa  Cin Nama yana kara yawaitar wari a jikin 'Dan Adam - Masana

Ana kiran wannan dan itacen da suna daban daban a fadin Najeriya, Agwaluma dai shine sunan da ake kiranta da yaren Hausa, Utieagadava a yaren Urhobo; Agbalumo a Yarbanci; Udala a Ibo, Efik a Ibibio; Ehya a Igala.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020