Gwamnonin Arewa sun yi kira da a soke Kwangilolin tituna da ba a kammala ba

Karatun minti 1
Gwamnonin Arewa

Gamayyar gwamonin arewacin Najeriya sun yi ga gwamnatin tarayya da ta gintse kwangiloli na aiki tituna da ta wandanda ba a kammala ba daga hannun ‘yan kwangila.

Kungiyar gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya ne suka yi wannan kira yayin wani taro da suka gudanar a  jihar Borno.

Gwamnonin sun ce ya kamata gwamnati ta kwace ayyuka daga ‘yan kwangilar da suka gaza ta kuma bai wa wadanda za su iya yin ayyukan cikin lokaci kankani domin samar da alfanu ga al’ummar yankin.

Taron da aka gabatar a birnin Maiduguri na jihar Borno, ya samu halartar gwamononin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe.

Yayin fitar da sakon kungiyar, shugaban taron, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zullum, ya yi kira ga jami’an tsaro da su sake dage dantse wajen cigaba da yaki da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

Kazalika kungiyar ta yi kira ga ma’aikatar albarkatun ruwa da su ja ruwan tafkin Chadi wanda a cewar kungiyar al’umma da dama suna amfana da shi.

Sun kuma bukaci da a shigo da jami’an ‘yan sanda wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog