Gwamnatin tarayya za ta kashe tiriliyan 2.3 wajen samar da lantarki a kauyukan Najeriya

Karatun minti 1
Farfesa Yemi Osinbajo - dabofm
Farfesa Yemi Osinbajo - Mataimakin shugaban Najeriya (APC)

Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya za ta kashe kimanin Naira titiliyan 2.3 domin samar da hasken lantarki a kauyukan Najeriya a karkashin shirin Solar Home Systems (SHS).

Ya bayyana haka ne a cibiyar kasuwanci da masana’antu ta jihar Lagos ‘LCCI’.

Ya ce shirin zai samar da cibiyoyin sarrafa hasken wutar lantarki da gidaje miliyan 5 a fadin Najeriya.

Ya ce samar da kananun cibiyoyin zai sanya a kalla mutane miliyan 25 amfana da hasken lantarkin a kauyukan da suke fadin Najeriya gaba daya.

Ya ce, “Muna da zummar fara aikin da wuri, duba da cewa, sanya cibiyar sarrafa hasken ranar zuwa lantarki a gidaje miliyan 5 ba karamin aiki bane, dole a fara da wuri.”

A cewarsa, shirin zai taimakawa ‘yan kasuwa wajen bunkasa bunkasar kasuwancinsu tare da taimakawa kamfanunuwan magunguna musamman a irin wannan lokaci don samar da kayan yaki da cutar COVID-19.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog