Home LabaraiHalin da ake ciki yanzu ya nuna babu shugabanci a Najeriya – Buba Galadima

Halin da ake ciki yanzu ya nuna babu shugabanci a Najeriya – Buba Galadima

by Dabo Online
0 comments

Jaipur, India (DABO FM) – Alhaji Buba Galadima, babban mai hamayya da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewar Najeriya ta tsinci kanta a yanayi na rashin shugabanci.

Buba Galadima ya ce bisa matsalar rashin tsaro da ta ta’azzara musamman a kwanakin nan da ‘yan bindiga dadi da mayakan Boko Haram suke cin karensu ba babbaka a arewacin Najeriya.

Ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da sashin HAusa na gidan Rediyon DW wanda DABO FM ta saurara.

“Yanzu ka dubi abubuwan da suke faruwa a Faskari, ‘Yan Tumaki, Jibiya, Batsari, Jihar Sokoto da Zamfara, yanzu fisabilillahi za ka ce akwai gwamnati a Najeriya? Ko akwai mai kishin al’umma a Najeriya?

“Ga bashi bila’adadin da Allah ne kadai Ya san iyakars kuma babu aiki guda daya da za a nuna wannan gwamnati ta yi. Shin idan mutum ya soki wannan sai ace yana kin gwamnati?

Kazalika da yake tsokaci kan zamanin mulkin Janar Sani Abacha, Buba Galadima ya ce gwamnatin Abacha ba sa’ar gwamnatin Buhari bace ta fuskar sha’anin mulki da ayyukan cigaban kasa.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00