/

Hamisu Breaker ya shiga jerin manyan mawakan da akafi kallo a Najeriya

dakikun karantawa

Fitaccen mawakin Hausa, Hamisu Breaker, ya zama wanda akafi kallon wakokinshi a duk cikin mawakan Hausa a halin yanzu.

DABO FM ta tattara bayanai wanda zamuyi duba akan Youtube inda a nan ne akafi kallon wakokin bidiyo a fadin duniya baki daya.

Zamuyi duba a kan jadawalin wakoki 100 da Youtube ya fitar da suka nuna wakokin da sukafi fice kuma akafi kalla sama da kowanne a Najeriya cikin wannan makon.

Daga cikin wakoki 100 na mawakan da suka hada da Wizkid, Davido, Burna Boy, Naira Marley da sauransu, wakokin Hamisu Breaker guda 9 ne suka fito a cikin jadawalin.

Duk da fitar da sabuwar waka mai sunan Dabo Dabo da Adamu Zango yayi, bata samu shiga sahun wadanda akafi saurara ba.

Daga cikin wakoki tara na Hamisu da suka fito akwai; Nagane Duniya wacce itace take a mataki na 16 cikin wakoki 100 a Najeriya, saman mawaka irinsu Rudeboy Psquare, Yemi Alade, Adekunle Gold, 2 Face , Kizz Daniel da sauransu.

Ga jerin wakokin Hamisu da suka fito a cikin jadawalin;

Nagane Duniya – Mataki na 16

Karshen Kauna – Mataki na 29

So Dangin Mutuwa – Mataki na 33

Tubali – Mataki na 38

Jarumar Mata – Mataki na 40

Bakan Gizo – Mataki na 68

Matata – Mataki na 84

Daga Yarda – Mataki na 89

Mai tafiya – Mataki na 92

Sauran wakokin Hausa da suka fito a jadawalin;

1. YNS Daso Samu ne – Mataki na 48

2. Aminu Ala- Chigari Tsakure 1 – Mataki na 80

Bisa ga wannan, idan ‘yan Najeriya miliyan 200 zasu hau Youtube, ya zamana cewar a cikin wannan makon an kalli wakokin Hamisu Breaker sau miliyan 8.

Karin Labarai

Latest from Blog