Labarai

Har yanzu babu ranar komawa makarantu – Ma’aikatar Ilimi

Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya ta ce har yanz babu ranar da aka fitar domin komawa makarantu.

Hakan na zuwa bayan da wasu gidajen labarai suka fitar cewar ranar 13 ga watan Yuni, za a koma makarantu a Najeriya.

Da take karyata labarin, ma’aikatar Ilimin a shafinta na Twitter, ta ce labarin kanzon kurege ne domin har yanzu bata yanke ranar da za a koma makarantu ba.

Hakazalika ma’aikatar tace ayi watsi da dukkanin abinda gidajen jaridun suka rawaito, ta kuma ce itace kadai ke da hakkin sanar da ranakun komawar.

Karin Labarai

UA-131299779-2