Sheikh Gumi
Taskar Malamai

Sheikh Gumi ya sake jaddada bidi’anci azumin ‘Sittu Shawwal’

RAJASTHAN: Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, malamin addinn Islama a Najeriya, ya sake jaddada bidi’ancin yin azumin ‘Sittu Shawwal’ bisa fahimtar Imam Malik (Allah Ya kara yadda a gareshi), kamar yadda ya ayyana.

Cikin wata hira da yayi da sashin Hausa na DW wanda DABO FM ta kalla, malamin ya bayyana cewar maganar bidi’ancin azumin ba fatawarshi bace, fahimta ce ta mazhabar Imam Malik da ake amfani da ita a Najeriya.

Tin a shekarar 2019, DABO FM ta fitar da rahotan yada malamin ya bayyana bidi’ancin azumin sittu shawwal, lamarin da ya sanya malamai suka yi masa raddi, ciki har da Sheikh Bn Uthman na jihar Kano in da ya kira fatawar da jahilci.

Sai dai a martanin da malamin ya yi, yace; “Daa a kasar nan, bamu san maganar azumin sittu shawwal ba saboda babu shi a mazahabar Imam Malik. Sai da yaran nan suka je kasar Saudiyya sannan suka dauko suka kawo mana, su kuma kasar Saudiyya mazahabar Imam Hambali suke bi.”

“Abin nan kuma ba ni na fada ba, hasalima littafi nake karanta wa a lokacin. A duba cikin littafin Muwadda Malik.”

Karanta mukalaloli tsakani malaman akan Sittu Shawwal daga kundin ajiyar DABO FM na 2019

‘Azumin Sittu Shawwal ba shi da asali, yin shi Bidi’a ne – Sheikh Gumi.

Jahilci ne baƙiƙƙirin wani jahili yace azumin ‘Sittu Shawwal’ ba Sunnah bane – Bn Uthman Kano

Karin Labarai

UA-131299779-2