//
Sunday, April 5

Har yanzu matsayin Jarumawan Arewa bai kai a nuna wa duniya ba – Naziru Ziriums

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Fitaccen dan Jarida dake aiki da sashin Hausa na Muryar Amurka, Nasir Ahmad Hausawa wanda aka fi sani da Ziriums, yace har yanzu da sauran jarumawan Arewa.

Zirium ya bayyana cewa “Jaruman Arewa, har yanzu basu kai inda ake so su kai ba ballantana su taimakawa wani.”

Ya bayyana haka ne yayin da yake martani a rubutun Dangalan Muhammad Aliyu akan abinda ya shafi tallafawa matasan Arewa don samun daukaka daga wata baiwa da Allah ya basu.

Dangalan yace; ” Ina ganin rashin masu daga darajar mawakan Arewa ne ya kawo mutuwar matasan dake tasowa, sannan kuma su jarumawan namu basa agaza musu ko da su daura su a shafinsu na sada zumunta.”

Masu Alaƙa  Zamani Riga: Me duniyar Kannywood take ciki a Yau da nasarorinta?

Anan ne Naziru Hausawa yayi maratani da cewa; “Dangalan ba magana ake ta daurasu a kan shafin sada zumuntar su ba.”

“Su kansu jarumawan Arewa basu kai inda ake so su kai ba tukunna balle su taimakawa wasu.”

“Ana musu wani kallon cewa sun kai, amma basu kai ko ina ba, ba abinda suke dashi. Wannan shine matsala.”

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020