Labarai

Sanata Wamakko zai gina katafariyar Jami’a a jihar Sokoto

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arerwa, Aliyu Wamakko ya kammala shirye-shirye domin gina katafariyar Jami’a mai zaman kanta a jihar ta Sokoto.

Rahotanni sun bayyana cewa tini dai Sanata ya cika dukkanin takardu zuwa ga hukumar dake kula da Jami’i’on Najeriya ‘NUC’ domin yin nazari da yin duba domin bada iznin ginin jami’ar.

Sashin Hausa na Legit.ng ya rawaito cewa; a yayin ziyarar tsohon gwamnan zuwa ofishin hukumar ta NUC ya bayyana manufarshi ta kafa Jami’ar cewa; “Zai yi ne domin cigaban Matasa” musamman duba da cewa Jami’o’i masu zaman kansu guda 3 a yankin arewa maso gabas.

Ita ma a nata bangaren, hukumar NUC ta hannun shugabanta Farfesa Abdulrashid, ta yaba masa wajen yin tunanin kafa Jami’ar tare da alkauranta bashi dukkanin wata gudunmawa wajen tabbatuwar Jami’ar.

Karin Labarai

Masu Alaka

Ganduje na cikin jerin gwamnonin dake fuskantar barazanar tsigewa daga kotun ƙare kukan ka

Muhammad Isma’il Makama

Rikici ya barke tsakanin Bafarawa da Wamakko a filin jirgin sama na Sokoto

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2