Home LabaraiMahaifin Umar M Shareef ya rasu

Mahaifin Umar M Shareef ya rasu

by Dabo Online
0 comments

Mahaifin fitaccen mawakin wakokin Hausa na zamani, Umar M Shareef, ya rasu a ranar Litinin, 2 ga watan Maris 2020.

Mawakin ya wallafa a shafukanshi na sada zumunta a daren Litinin tare da rokon addu’ar al’umma domin neman yafiyar mahaifin nashi.

DABO FM ta tattara cewar mahaifin mawakin ya kasance mahaifin daya daga cikin jarumawan masana’antar Kannywood, Abdul M Shareef wanda kani ne ga Umar Shareef.

Umar M Shareef ya kasance fitaccen mawakin fina-finan Hausa na Kannywood wanda yayi shura wajen iya rera wakokin soyayya.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00