Labarai

Haramcin shiga Amurka ga yan siyasar da sukayi madugin zabe zai shafi iyalansu -Amurka

Kasar amurka ta bayyana cewa haramci shiga kasar da tayi wa wasu ‘yan siyasa a Najeriya da sukayi magudi ko tada zaune tsaye a lokutan zabe zata shafi iyalansu.

DABO FM ta binciko cewa kasar dai tace “Ta ta soke izinin hatta wadanda ta riga da ta baiwa izinin shiga kasar a baya.

A ranar Talata dai gwamnatin kasar Amurka tace ta haramtawa wasu yan siyasar Najeriya shiga kasar a shirin da take na hadin gwiwa da gwamnatin Najeriya wajen yakar cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da Dimokradiyya.

Haka-za-li-ka, gwamnatin Amurka da take karin amsa tambayar da jaridar Punch tayi mata tace; haramcin shiga kasar zai shafi iyalan ‘yan siyasar da ta ayyana haramtawa shiga kasar “Da zarar an sanyawa dokar haramcin hannu.”

Zamu sanar da duk wanda sunanshi a fito cewa mun soke izinishi na shiga kasar Amurka (Ga wadanda kasar ta riga ta bawa izinin shiga).

“Duk wanda sunansu ya fito a jerin, baza mu basu izinin shiga kasar Amurka ba idan sun nema.”

“Da zarar an fara sanyawa dokar hannu, haramcin zai shafin iyalan wadanda sunayensu suka fito.

Sai dai kasar Amurka ta shaidawa jaridar Punch cewa bazata bayyanawa duniya sunayen mutanen ba, bisa dokarta ta tattara sirrikun mutane.

Ta tabbatar da cewa duk wadanda hukumomin sa ido na duniya suka tabbatar da sun kawo hargitsi ko yin magudi a zaben 2019 ne suke a jerin sunaye.

Karin Labarai

Masu Alaka

An dauke wuta a birnin New York na kasar Amurka a karon farko cikin shekaru 42

Dabo Online

Za a tsige shugaba Donald Trump

Rilwanu A. Shehu

Yakin Duniya III: Majaisar Iraqi ta yanke hukuncin fatattakar sojojin Amurka daga kasarta

Muhammad Isma’il Makama

Yadda za mu kare kan mu daga kamuwa da cutar zazzabin ‘Lassa’ -Dr Abdul’aziz T. Bako

Muhammad Isma’il Makama

Yanzu-Yanzu: Mahaifin matashin da baturiya ta biyo Kano zai kai maganar gaban jami’an tsaro na ‘SSS’

Muhammad Isma’il Makama

Masana a Amurka sun gano yin azumi sau 2 a mako na kara tsawon rai da riga-kafin cututtuka

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2