//
Thursday, April 2

Ku haramta kungiyar Shi’a – Kotu ta umarci gwamnatin tarayya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kotu ta umarci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta haramta kungiyar ‘Yan uwa Musulmi ta Najeriya dake bin mazahabin Shi’a.

A ranar Juma’a, wata babbar kotu a Abuja ce ta yanke haramta kungiyar biyo bayan zanga-zangarsu da kotu dace ta addabi garin na Abuja.

DABO FM ta rawaito daga Jaridar Punch ta ranar Asabar cewa; “Mai shari’a Nkeonye Maha ce ta bayarda umarnin tare da bayyana dukkanin al’amuran kungiyar a fadin Najeriya “Aikin ta’addanci da fafutuka ba bisa ka’ida ba.”

Kotu ta kuma haramta tare da dakatar da “Wani ko wata kungiya” daga tsoma hannu ta kowanne fanni cikin abinda ya shafi kungiyar ta IMN a kaf fadin tarayyar Najeriya.

Haka zalika dai kotu ta umarci ofishin ministan Shari’a na Najeriya da fitar da rubutacciyar doka a gwamnatance akan haramta kungiyar ‘yan Shi’ar tare da wallafawa a manyan jaridun kasa guda 2.

Masu Alaƙa  Buhari zai ciwo bashin dalar Amurka miliyan 890 domin yaki da sauro

Alkaliyar ta bada unarnin ne biyon bayan bukatar yin hakan daga gwamnatin tarayya.

Jaridar Punch ta tabbatar da ganin takarda mai lamba FHC/ABJ/CS/876/2019 da ofishin ministan shari’a na kasa ya shigarwa kotu.

Tunatarwa: Shigar da kara daga bangaren daya ba tare da ji daga daya bangaren ba, shine ma’anar Ex-Parte

Kungiyar IMN ce wacce ake tuhuma akan karar da ofishin ministan ya shigar daga babban sakataren ofishin, Mr Dayo Apata. Sai dai bisa kasancewar karar zama “Ex-Parte” babu wakilin kungiyar Shi’a da ya wakilceta a zaman kotun.Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020