Taskar Malamai

Harbe-harbe a gidan Sheikh Dahiru Bauchi ya jikkata mutane 2

Sheikh Dahiru Bauchi, mataimakin shugaban Fatawa a Najeriya, ya bayyana yacce ta kasance biyo bayan rahotannin harbe-harbe da aka samu a gidanshi.

Sashin Hausa na Legit.ng ya rawaito daga Jaridar Daily Trust cewa; “Alhamis, 12 ga watan Satumba yayin da yake ganawa da jama’a a gidansa, inda yace rashin jituwar kuwa ta auku ne tsakanin Yansandan dake gadin gidansa da kuma wani bako da ya yi kokarin shiga gidan.”

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dahiru Bauchi yana cewa: “Da wannan mutumi ya nemi ya shiga gidana sai Yansandan dake gadi suka hana shi shiga sakamakon basu gamsu da shi ba, wannan ne ya kawo cacar baki tsakaninsu, har Yansandan suka yi harbi domin su tsorata mutumin.

“A dalilin haka suka ji ma mutane biyu rauni, a yanzu haka mutum daya na asibiti yana samun kulawa, yayin da dayan kuwa har ma an sallameshi.” Inji shi. – Legit Hausa

Malamin yayi kira da masu yada jita-jita na cewa an kaiwa masa hari da sani abinda suke yadawa ba gaskiya bane.

Karin Labarai

UA-131299779-2