//
Wednesday, April 1

Bazamu kara gallazawa ‘Yan Najeriya ba – Buhari

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaba Muhammadu Buhari yayi albashi ga ‘yan Najeriya cewa gwamnatin shi ta ‘Next Level’ bazata kara gallazawa yan Najeriya ba.

Shugaban ya bayyana haka ne yayi wata ganawa da Kungiyar Masu Kananun sana’o’i wanda shugaban Quadri Olaleye, ya jagoranta a fadar gwamnatin dake Abuja.

A sanarwar da mataimakin shugaba Buhari a fannin yada labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar, ta bayyana cewa gwamnatin zata cigaba da samo duk wata hanya da zata rage wahal-halun da ‘yan Najeriya suke fama da su.

Ya kuma kara bayyana gwamnatin zata cigaba da kokarin samawa yan Najeriya jin dadi kasarsu.

“Akan batun farashin Mai, Na yarda da ku cewa akwai bukatar kawo karshen cin hanci da rashawa da rashin kwazo dake a wannan bangaren.”

Masu Alaƙa  El-Rufa'i yayi tir da kashe Tiriliyan 17 a gyaran wutar lantarki da gwamnatin Buhari tayi

“A matsayin gwamnatin, ina tabbatar kuma da cewa bamu da wata niyyar kara wahal-halun da ‘yan Najeriya suke ciki.”

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020