A gaggauce: DABO FM ta rasa ma’aikaci sakamakon hatsarin babur a jihar Kaduna

Karatun minti 1

Sashin DABO FM dake wallafa mujallar mako mai taken Taskar Dabo ya rasa hazikin ma’aikaci, Abubakar Ibrahim wanda aka fi sani da Hassan dan asalin jihar Kaduna.

Ya rasu a ranar Laraba sakamakon hatsari da ya rutsa da shi a kan hanyar shi da komawa gida bayan tashi daga ofishin Taskar Dabo da yammancin Laraba.

Kafin rasuwarshi ya kasance mai kula da sabon ofishin Jaridar Taskar Dabo da ake shirin kaddamarwa a jihar Kaduna, ofishi mai lamba 2 ABU Staff Quaters Zaria.

An haifi Marigayi Abubakar Ibrahim a ranar 20 ga watan Fabarairun 1992 a unguwar Kakaki cikin birnin Zariya, ya yi karatun Firamare a makarantar Firamare ta Alfitra dake garin Zaria in da ya yi Sakandire a Kwalejin Barewa.

Ya yi karatunsa na Diploma a Nigeria Institute of Leather and Science Technology da ke a Samaru cikin Zaria, yana sake yin babbar Diploma a makarantar ya yin da Allah Ya dauki rayuwarsa.

Ya rasu ya bar mahaifinsa, Alhaji Ibrahim Auwalu, dan uwa ga shugaban Gidan Rediyon Najeriya Kaduna, Alhaji Buhari Auwalu, da mahaifiyarsa da sauran ‘yan uwa.

Daukacin DABO FM ta masu hulda da mu, muna mika sakon ta’aziyyarmu da iyalan mamacin da amininsa, Mu;azu Abubakar Albarkawa, shugaban jaridar Taskar DABO tare da daukacin al’ummar Musulmi baki daya, da fatan Allah Ya gafarta masa Ya sa aljanna ce makomarsa, mu ma kuma in ta mu tazo, Allah Ya sa mu cika da imani.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog