Hasken Rayuwa: Dabi’un Musulmi bisa koyarwar Manzon Allah S.A.W

As Salam ‘Alaikum wa Rahmatullah wa Barakaatuh. Godiya ta tabbata ga Allah, muna masa godiya muna neman taimakonsa muna nema gafararsa, muna neman tsarinsa daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu.

Wanda duk Allah SWT ya shiryar, to babu me ɓatar dashi, wanda duk kuma ya ɓatar, to babu me shiryar dashi.

Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah haka kuma ina shaidawa cewa annabi Muhammad bawansa ne kuma manzonsa.

Bayan haka; ‘yan uwa masu albarka, kamar yadda aka buqaceni da yin rubutu kan abinda ya shafi addininmu da kuma rayuwarmu ta yau da kullum (a bisa koyarwar manzon Allah SAW) wanda -InshaAllahu- ni da farko me rubutu, da dukkan al’umma musulmi zamu amfana dashi baki daya.

Toh kasancewar nayi rubutun ba tare da ambatamin maudu’i da zanyi magana akanshi ba, naga ya kamata na za6i abinda ya shafi mu’amala da dabi’u da halaye kyawawa na musulunci a bisa hasken koyarwar manzon tsira Annabi Muhammad (SAW).

Da farko dai kamin mu shiga cikin maudu’in namu wanda ze kasance gajere InshaAllahu kasancewar rubutun zai zama Bi-Da-Bi (wani bayan wani), saboda gujewa tsawaitawa da kuma kasancewar maudu’in me fadi da girma, matuƙa gaya.

Tabbas wannan maudu’i yana da matuqar muhimmanci ga al’ummar Musulunci a ko ina take.

Masu Alaƙa  Dabi'un Musulmi bisa koyarwar Manzon Allah S.A.W, Daga A. Bin Uthman

Ya ishemu sanin muhimmacin kyawawan dabi’u da halaye na gari kasancewar Allah SWT daya tashi yabon manzonsa SAW seya ce (Al-Qalam, 68-4): (Kuma tabbas kai [annabi Muhammad SAW] kana kan dabi’u [da halaye] masu girma [da daukaka da daraja]).

Haka zalika yace SWT (As-Shams, 91-9,10): (Tabbas yaci nasara wanda duk ya kyautata ta [zuciya, wadda itace ma6ubbugar halaye na gari, idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru] kuma yayi hasara [ya ta6ar6are ya lalace] wanda duk ya wulaqanta ta [ya munanata]) haka ayoyi da dama sunyi magana kan halaye masu kyau wanda inshaAllah idan ana biye za’a ji ambatonsu da bayaninsu a bisa hasken ilimin magabatanmu -Allah ya musu rahama.

Haka kuma cikin hadithai cewar manzon tsira SAW
(Musnad I. Ahmad, M. abi hurairah, 8952. Da Muwatta Malik, 2632/3): (An turoni domin na kammala kyawawan dabi’u [cikin al’umma]), haka abu zarr (cikin abinda Ibn Abbas ya ruwaito) -kamin musuluntarsa- yayin da ya aika dan uwansa domin ya bincika gaskia gameda aiko annabin Allah, dawowar dan uwannasa seya ce masa, “na sameshi yana kira ga kyawawan dabi’u” (Bukhari, 3861. Muslim, 2474).

Masu Alaƙa  Dabi'un Musulmi bisa koyarwar Manzon Allah S.A.W, Daga A. Bin Uthman

Haka hadithai jan hakan suna da yawa, sedai ba kawosu gaba daya ne abin buqata ba, sedai samun darasi daga abnd ya samu.

Daga cikin falaloli da wadannan halaye suka qunsa; kasancewar Allah subhanahu wata’ala ya girmama wannan al’umma ta annabi Muhammad SAW ta hanyar saka halaye masu kyau cikinn abinda yake ibadah ake samun lada kansa, bal cikin manya-manyan ibadu da bawa zeyi domin kusantar ubangijinsa.

Abdullahi Bn Amr -RA- ya ruwaito cewa, Manzon Allah -SAW- yace: (mafi alkhairinku shine me kyawawan dabi’u) (Sahih Muslim, 2321).
Haka uwar mu’minai -A’isha R.A- ta ruwaito cewa taji manzon Allah SAW yana cewa: “tabbas mu’mini ze (iya ya) kai daraja/matsayin me azumi da sallah (qiyamullaili), saboda kyawawan dabi’unsa” (Sunan Abi Dawood 4798. Sahih). Hakazalika abu hurairah ya ruwaito cewa, manzon Allah SAW yace: “Mu’mini daya fi kowane Mu’muni cikan i
mani shine me kyawawan dabi’u” (Sunan Abi dawood, 4682. Sahih).

Haka Abu umamata Al-baahily ta ruwaito cewa manzon Allah SAW yace: “… Ni me daukan nauyi da tsaya ma -dukkanin wanda ya kyautata dabi’unsa da halayensa- wani gida a chan saman qololuwar Aljannah (ko kaman yanda ya fadi SAW)”(Sunanu Abi dawood, 4800). Haka hadithai kuma masu matuqa da dimbin yawa suke nuna falala da muhimmanci na Halayya masu kyau.

Masu Alaƙa  Dabi'un Musulmi bisa koyarwar Manzon Allah S.A.W, Daga A. Bin Uthman

Tambaya! Shin mutum ze zaɓi wasu ne da ranshi ya masa ya bar wasu cikin wadannan halayen qwarai da addini ya koyar (wadanda zamu fadesu daya bayan daya da falalarsu)?

Shin idan mutum yayi qoqarin gyarawa me wani sakamako ze samu?

Shin idan mutum ya nisanci wadannan halaye me yake janyo ma kansa?

Shin akwai wata nasara ta rayuwa dunia da lahira data wuce mutum ya kyautata halayensa?

Don sanin amsoshin wadannan tambayiyi da wasunsu da yawa da qarin bayani, se a gamu damu a rubutunmu na gaba wato “Jumu’a ta zagayo na biyu 2” InshaAllahu.

Dimbin godia abisa lokacinku da nutsuwarku. Ina kuma neman afua abisa tsawaitawa saɓanin yanda a kayi niyya a farko.

Wa Sallallahu Wa Sallama Alaa Nabiyyina Muhammad Wa Alaa Aalihibwa Sahbihi Wa Sallam.

Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya Bamu Ikon Kyautata Halayenmu Domin Cin Ribar Hakan Kusa Da Nesa.

•Dan uwanku a Musulunci✍🏼

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.