Wallahi zamu fara hukunta ‘yan sandan MTD bisa ci mana mutunci – Al’ummar Kabala Costain Kaduna

Al’ummar unguwar Kabala Costain dake arewacin jihar Kaduna, sun koka kan yacce yan sandan MTD na yankin suke ci musu mutunci.

A wani faifan bidiyo da ake baiwa manema labarai a shafukan sada sada zumunta musamman a manhajar Instagram. An hangi wani magidanci yana kokawa bisa irin cin mutuncin da ‘yan sanda suke yiwa iyayensu.

DABO FM ta tattaro cewa magidancin mai suna Alhaji Bashir daga unguwar Kabala Costain ya bayyana rashin jin dadinshi ga ‘yan sandan unguwar bisa cin mutunci wata Mahaifiya tare da ‘ya ‘yanta a ofishin ‘yan sanda.

Ya bayyana cewa hakan ya biyo baya ne bayan da jami’an ‘yan sanda suka cafke dan uwansu ba tare da samunshi sa laifin komai ba, hakan ya saka ‘yan uwan nashi zuwa ofishin domin bin bahasin kamun nashi.

A cewar Alhaji Bashir, zuwansu ke da wuya jami’an ‘yan sanda na MTD duka hau su da duka, zagi hadi da cin mutunci.

“Matar tazo da ‘yayanta, mata biyu da namiji daya, babban ‘danta. Haka suka rika dukansu suna wulakanta su.”

DABO FM ta rawaito cewa, mutumin yace ‘yan sanda suna ta cewa; Ko Buhari da El-Rufa’i ma babu abinda zasu iya yi musu.

“Abinda yafi bani mamaki ma, suna cewa ko El-Rufa’i ko Buhari ma, ba wanda ya isa yace zai musu wani abu.”

Daga karshe yayi kira ga hakumomi da cewa yakamata su dauki mataki domin tura ta fara kai su bango, har ma yace idan fa wadanda suka da hakki suka gaza daukar mataki, “To lallai zasu dauki doka a hannunsu.”

“Abinda nake kira shine, Idan gwamnati bata dauki mataki ba, toh Wallahi thumma Tallahi , mu al’ummar gari, zamu dauki mataki, zamu dauki doka a Hannu.

%d bloggers like this: