Hatsarin mota ya kashe mutane 9, jikkata 15 a Kano

Kimanin kusan mutum tara ne suka rasa rayukansu, inda 15 kuma suke gadon asibiti a wani hatsarin mota daya ritsa dasu a karamar hukumar Takai dake birnin Kano.

Hatsarin ya ritsa da matuka mota kirar Sharon mai lamba BUJ 389 AA- JGW da Toyota Sienna da lamba YLA 389 PK – Adamawa.

Direban Sharon ya fada hannun mai Toyota Sienna yayin kauracewa ramukan titin na karamar hukumar Takai, daga lokacin ne motocin biyu suka hade da juna.

A take mutun 9 suke mutu, sauran 15 kuwa tini an garzaya dasu babban asibitin garin na Takai domin karbar agajin gaggawa.

Jami’i mai hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi, ya bada tabbacin faruwar al’amarin.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.