Jihar Edo: ‘Yan sanda sunyi arangama da masu sakawa mata yaji a al’aurarsu

Rundunar ‘yan sandar jihar Edo tace tayi arangama da wasu matasa da ake zarginsu da sakawa wata mata yaji a cikin al’aurarta.

Matar da aka zarga da satar waya tace, an kaita wajen boka domin ayi mata asiri, lamarin da ya kai har an saka mata miciji a cikinta kafin daga bisani ta amsa zargin satar.

Sai dai tace ta amsa laifin ne domin a rabata da abin da aka saka mata, bayan da aka cire micijin ta kara musanta zargin, lamarin da yasa matasan suka fusata wanda har ya jawo suka kaita dakin wani Otal don su saka mata yaji a al’aurarta.

“Abinda yafi min ciwo, sun dauke ni bidiyon lokacin da suka min tsirara, sa’annan suka watsa min yaji a cikin farji na.”

Hukumar yan sandan jihar ta Edo tace da zarar ta gama bincike, zata aike matasa gaban kuliya domin fuskantar hukunci.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.