Sha’aban Sharada

Hon Sha’aban Sharada zai tura Dalibai 100 zuwa kasashen Waje yin Digirin farko

Bayan maganganu da suka bulla ‘yan kwanaki kadan cewa shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai ta najeriya Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada ya dauki nauyin kai dalibai 100 kasashen waje, wakilin Dabo FM ya bi kadin wannan magana.

Dabo FM ta gana da babban makusanci ga dan majalisar wakilai ta kasa mai wakiltar karamar hukumar birni, Hon Ibrahim Rabiu Tahir, wanda ya tabbatar mana da wannan maganar da cewa “Eh kwarai wannan magana akwaita.”

Hon. Ibrahim Rabiu Tahir wanda shine shugaban kasuwar Beruit dake kano kuma dan takarar majalisar tarayya a zaben daya gabata, ya kara da cewa “Kwanaki kadan da suka wuce ma munyi ganawar sirri akan wannan hobbasa tare da wadanda muka dora wa alhakin tantance daliban.”

“Yanzu bana gari bisa rashi da akai min amma ina tabbatar muku da abubuwa sunyi nisa kwarai da gaske, kuma zan sanar daku duk abinda ake ciki da zarar na dawo nan gaba.”

Masu Alaƙa  Har yanzu Abba Kabir Yusuf muka sani a matsayin dan takarar gwamnan PDP - INEC

A wani bincike da wakilin mu yayi ya gano gidauniyar dan majalisar ta raba fom ga ‘yan asalin karamar hukumar Birni, har daliban da suka samu wannan dama sun cike sun dawo dashi domin tantancewa.

A wani rahiton da jaridar Leadership ta fitar yace mai taimakawa dan majalisar, Faruk Malami Sharada ya shaida wa wakilimmu yayin raba fom ga matasan da akayi ranar Talata.

Ya ce, dan majalisar ya yi shiri dan bada tallafin karatu ga Matasa 200 da zai tura kasar Sudan da Chana.

“Dama tun kafin yakai wannan matsayi yana taimakawa cigaban al’umma ta fannoni da dama a yankin.”

Ya kara da cewa an bada fom dan tantance mutum 100 su je su yi karatun digiri na darussan kimiyya da fasaha da sauran fannoni.

Masu Alaƙa  Kano: Mutane 176 ne suka rasa ransu sakamakon hadarin jirgin sama a rana irin ta yau

“An yi anfani da ranar da kasar nan ta cika shekaru 59 da samun mulkin kai daidai da daya a watan Oktoba tare da yin tawassali da sunayen Ubangiji aka raba fom din da za’a tantance mutum 200 da za’a tura Sudan da Chana karkashin Gidauniyar Sha’aban Sharada.”

Faruk Malami yace a tsarin kason farko na mutum 100 za’a soma turawa Sudan a wannan tantancewa da ake.

Ya tabbatar da cewa wannan somin tabi ne kuma dori akan irin ayyuka da dan majalisar na karamar hukumar birni a tarayya Sha’aban Ibrahim Sharada yake da suka hada da bai wa dalibai Kwamfutoci da gyaran makarantu da masallatai da bada tallafin jari da sauran abubuwa da dama.

Masu Alaƙa  Kano: Ni yakamata a zaba - Muhammad Abacha

Kudurin dan majalisar shine ya fitatda dalibai 1000 yan mazabar karamar hukumar Birnin Kano kafin karshen zangon wakilcinsa.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.