//
Tuesday, April 7

Halayyar Buhari ta gaskiya ta bayyana bayan darewarshi shugabancin Najeriya – Buba Galadima

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Buba Galadima ya bayyana wannan ne a wata hira da ya yi a Jaridar New Telegraph inda yace da Buhari ya tsaya kan manufofin da aka san shi da su a baya, da Najeriya ta cigaba a mulkinsa. Injiniyan yake cewa Buhari ya samu abin da yake so na mulkin Najeriya bayan da ya hada kai da sauran bangarorin kasar.

Sai dai a cewarasa, bayan Buhari ya samu mulki sai ya fito a mutum. Galadima yace: “Shi Buhari ya san abin da ya kawo shi mulki, ya san irin sadaukarwar da wasunmu su ka yi domin ganin ya zama shugaban kasa, amma ya na samun mulki ya fatattake mu.”

Masu Alaƙa  Bana bukatar sasantawa tsakani na da Buhari - Buba Galadima

Buba Galadima yake cewa an yi watsi da duk wadanda su ka yi wa Buhari gwagwarmaya har ta kai aka tsare su da sunan sun ci amanar kasa. Galadima ya rike Sakatare na jam’iyyar CPC a 2011.

“Da mun bi tsarin da mu ka shirya a 2002, da yanzu Najeriya ta zama irin su kasar Indonesiya, Maleshiya, Singafo, Indiya da sauran kasashen da su ka cigaba.” Inji babban Jigon adawar kasar.

“Mun yi wa Buhari yakin shekara da shekaru, amma wannan bai sa ya zama shugaban kasa ba sai da ya tsallaka ya hadu da sauran yankunan Najeriya. Nan ya ci zabe, kuma aka gane halinsa.”

Masu Alaƙa  Gobe Alhamis, Buhari zai tafi kasar Saudi Arabia

A game da zargin PDP da kashe kasar nan da Buhari ya saba, Galadima yace “Mu yarda cewa da gaske ne an kashe kasar nan. Meyasa aka zabe shi? Ba an zabe sa ba ne domin ya kawo mafita?” Galadima ya tike da: “Wannan ba hujja ba ce da za a rika daura laifi a kan gwamnatocin baya.

Abin ya na bani dariya. A cikinsu, wanene bai cikin gwamnatin PDP, har shugaban kasan kansa.”

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020