Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi za ta dauki sabbin Ma’aikata

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, tana neman sabbin Ma’aikata.

DABO FM ta binciko cewa; Hukumar ta bayyana haka ne a shafinta na yanar gizo gizo inda ta baiwa dukkanin masu sha’awar neman aiki hanyar da zasu bi wajen neman aikin cikin sauki.

Ga ma’abota DABO FM, zasu gane cewa mun saba wajen nemo dammakin ayyukan yi, karatu kyauta da sauran na’o’in tallafin al’umma musamman Matasa.

NDLEA ta na neman ma’aikata don yi aiki a matsayin;

  1. Ma’aikaci mai kula da dangogin maguguna masu sinadarin ‘Narcotics.’
  2. Mataimakin mai kula da dangogin ‘Narcotics.’

Masu neman aiki mai lamba ta daya a rubutun sama, zasu kasance;

  • Masu shekaru: 22 zuwa 30.
  • Karatu: Digiri ko HND (Makarantun da ma’aikatar Ilimi ta aminta da ingancinsu kawai.)
  • Idan Likita ne ko Lauya: Digirinsu ya kasance ya shafi bangaren.

Game da masu neman aiki mai lamba ta biyu;

  • Shekaru: 18 zuwa 30.
  • Matakin Karatu: Sakandire zuwa sama.

Dukkanin ayyukan na din-din-din ne.

Masu neman aikin zasu tura takardunsu zuwa  www.emplug.com ko kuma a danna a hoton tambarin dake kasan wannan rubutun.

Za’a rufe shafin neman aikin a ranar 29 ga watan Agusta 2019.

Shawara: A nemi shagon ‘Cafe’ mafi kusa domin cike-ciken ya zama na na yayi dai dai.

Domin neman cikakken bayani, a zargazya https://www.ndlea.gov.ng/careers/ ko a danna a hoton kasa.

Danna anan don cikakken karin bayani

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.