Tsoho mai shekaru 60 ya yi wa Yarinya ‘yar shekara 10 fyade a jihar Imo

Rundunar ‘yan sandan Najeriya, reshen jihar Imo ta tabbatar da kamu wani mutumin mai shekaru 60 a duniya bisa zargin yi wa wata yarinya mai shekaru 10 fyade.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.

Jami’ian SARS ne suka kama tsohon da aka bayyana da sunan Onyekwere Umunna, dan asalin garin Achara ne dake karamar hukumar Obowo ta jihar Imo.

DABO FM ta binciko cewa tini dai tsoho Onyekwere ya amsa laifin yin fyaden da ake zargin ya aikatawa karamar yarinyar.

Kakkakin ‘yan sanda ya bayyana cewa da zarar rundunar ta kammala binciken da take yi, zata aike da tsohon zuwa gaban kuliya domin fuskantar hukunci dai dai da abinda ya aikata.

Sanarwar tace; “A ranar 6 ga watan Agusta na shekarar 2019 da misalin karfe 5:45 na yamma, jami’an SARS, suka damke wani Onyekwere Umunna, mai shekara 60 wanda aka zargin da yiwa karamar yarinya fyade.

“Mutumin ya amsa laifinshi, inda aka garzaya da yarinyar zuwa Asibiti domin kula da

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.