EL-Rufai ya gindaya tsauraren sharuda 7 kafin amincewa da tafiyar Al-Zakzaky kasar Indiya

Gwamnatin jihar Kaduna a karkashin gwamna Mallam Nasiru El-Rufa’i ta zayyana sharuda 7 da za’a cika kafin ta amince da tafiyar Zakzaky zuwa kasar Indiya neman lafiya.

DABO FM ta tabbatar da cewa ; Kwamishan harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan, a wata takarda da ya fitar ta bayyana sharudan da gwamnatin ta gindaya shugaban haramtacciyar kungiyar IMN.

A ranar 5 ga watan Agusta ne dai babbar kotu a jihar Kaduna ta amince da bukatar Sheikh Zakzaky na ketarewa kasar Indiya domin kula da lafiyarshi.

Ga jerin sharudan;

Har sai:

  1. Ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje ta tabbatar da zuwan ganin Likitan da Sheikh Zakzaky zai yi a asibitin Medanta na kasar Indiya.
  2. Sun amince kuma sun rubuta takarda tabbatar da dawowarsu Najeriya don cigaba da shari’a da zarar an sallamesu daga asibitin tare da cewa su da kansu zasu dauki nauyi tafiyar da kudinsu.
  3. Sun kawo sanannin mutane guda 2, daya ya kasance Sarki mai daraja ta daya, dayan kuma ya kasance babban mutum kuma sannan a cikin jihar Kaduna tare da nuna shaidar mallakar fili/muhalli a jihar ta Kaduna.
  4. Gwamnatin tarayya ta karbi shaida daga kasar Indiya akan cewa babu wanda zai shiga tsakani, kuma bazata karbi bukatar su Zakzaky su mika kansu a matsayin ‘yan gudun Hijira ba.
  5. Jami’ain tsaron Najeriya zasuyi musu raki tare da kasancewa da su a duk wani motsi da zasuyi.
  6. Ofishin Jakadancin Najeriya a kasar Indiya ya bada tabbacin cewa zai kula dashi tare da babu wanda zai ganshi ko ya kawo masa Ziyara ba tare da sahalewar ofishin ba.
  7. Sun bada tabbaci a rubuce tare da sa hannun lauyoyinsu cewa bazasu kawo wa shari’arsu tsaiko ko yin wani abu daya sabawa dokar Najeriya da Indiya ba, a yayin zamansu a kasar ta Indiya.

Daga karshe gwamnatin ya bayyana cewa bisa sharudan da kotu ta ayyana wa Zakzaky ya sa gwamnatin ta daukaka domin neman karin sharuda wanda gwamnatin ta gindaya.

Tin a ranar Talata, shugaban kula da hukunce-hukuncen shari’a na gwamnatin jihar, Mista Dari Bayero, ya bayyana cewa a ranar Laraba gwamnatin za ta daukaka kara.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.