Fitaccen jarumi da mawakin Hausa, Adam Abdullahi Zango ya koma masana’antar Kannywood, masana’antar da a baya ya ayyana ficewa daga ciki.
DABO FM ta tattara cewar jarumin wanda aka fi sani da A. Zango ya fita daga Kannywood a watan Augustar 2019.
Zango ya bayyana komawarshi zuwa masana’antar ne bayan ya wallafa takardar rijista da ya cike ta hukumar tace fina-finai ta jihar Kano a shafinshi na Instagram.
Adamu yayi furucin “An wuce wurin”, kana ya cigaba da tallata sabuwar wakarshi mai sunan Dabo Dabo.
Yayin bin martani daga masu bibiyarshi sukayi a shafin, DABO FM ta tattaro kalaman wasu daga cikin ‘yan masana’antar da suka bayyana farin cikinsu bisa matakin jarumin.
Daga cikin jaruman akwai Ado Gwanja inda ya bayyana cewar; “(Wallahi x3), na fika farin ciki, Adam Zango, Alhamdulillah.”
Wannan ba shine karo na farko da jarumin yake magana kuma yake janye wa ba.
Ku bayyana ra’ayoyinku a shafinmu na Facebook, Dabo FM.