Labarai

Hukumar ‘Yan sanda zata dauki ma’aikatan wayar da kan Jama’a guda 40,000 – IGP Adamu

Babban sifetan yan sanda na Najeriya, Muhammad Adamu, ya bayyana cewa hukumar yan sanda a wannan lokacin da yake jagoranta ta kammala shirin fito da ‘yan sandan wayar da kan Al’umma.

Ya bayyana cewa za’a dauki ma’aikata dubu arba’in a bangaren wayar da kan Al’umma inda kuma zasu kasance masu matsayin kwastabul na musamman.

DABO FM ta binciko cewa babban sifetan ya bayyana haka ne a wani taro da yayi ranar Talata tare da manyan jami’an rundunar a ofishinsa dake Abuja.

IGP Adamu yace; “Za’a dauki ‘yan sanda wayar da kan ne a kalla guda 50 daga kowacce karamar hukuma 774 da ake dasu a Najeriya.”

Ya kara da cewa kowanne dan sandan zai yi aiki ne a wurin da yake rayuwa.

“Za’a dauki ‘yan sanda 1,400 daga Kungiyoyin Addinai, Kasuwanni, masu ababen hawa, Mata, Matasa, ‘Yan Kasuwa tare da malaman makaranta domin samun wakilci daga dukkanin sassan al’umma.

Karin Labarai

Masu Alaka

IGP: Za’a dauki ‘yan Sandan sa kai 50 a kowacce karamar hukuma

Rilwanu A. Shehu
UA-131299779-2