Labarai

Arewa ta samu karuwar masu digiri na biyu sama 30 daga Jami’a daya a kasar Indiya

‘Yam Najeriya sama da 30 ne suka kammala karatunsu a wata Jami’a dake arewacin kasar Indiya.

DABO FM ta binciko cewa ‘yan Najeriyar sun kammala karatun nasu a jami’ar NIMS dake jihar Rajasthan a kasar ta Indiya.

Wakilin DABO FM dake kasar Indiya ya tabbatar mana da cewa; dalibai yan Najeriya da adadinsu ya kai guda 30, sun kammala karatun nea fannoni daban wadanda suka hada da harklar Lafiya, Kimiyya da Fasaha, Ilimin Kwamfuta, Kasuwanci, Fannin Tattalin Arziki da sauran manyan fannoni na yau da kullin.

An dai gudanar da bikin kammala karatun daliban kasashen waje da sukayi karatu a jami’ar ne kadai, a wani salo na nuna ban girma da daraja daliban a ranar Talata 29 ga watan Yuli.

Da yake jawabi, shugaban jami’ar, Farfesa Balbir S Tomar, wanda ya samu wakilcin Maga-takardar jami’ar ya bayyana jin dadinshi bisa kammala karatun da sukayi tare da yi musu fatan alheri a sabon babin rayuwarsu da suka bude.

Daliban da suka fito daga jihohin Adamawa, Bauchi, Kaduna, Kano, Katsina, Jigawa da birnin tarayyar Abuja.

Da muke zantawa da daya daga cikin daliban, Ibrahim Sa’id Noboi, dan asalin jihar Adamawa ya bayyana irin farin cikin da suka kasance a dai dai lokacin gudanar da bikin yayesun.

Karin Labarai

Masu Alaka

Saurayi ya kashe kanshi bayan zargin fyade

Dabo Online

Matsalar Tsaro: Akwai buƙatar a tuna maka Baba, Daga Rabi’u Biyora

Dabo Online

Matasa sun kone motocin APC a Abuja

Dabo Online

Wani mutum ya kwarara wa wasu matasa 8 ruwan batir a jihar Anambra

Dabo Online

Matasan jihar Kano sun fara zanga-zangar kin amincewa da ƙarin masarautu 4 a jihar

Dabo Online

Sulhun shafaffu da mai a karamar hukumar Fagge

Dabo Online
UA-131299779-2