//
Thursday, April 2

Kotun koli ta kwace zaben dan majalissar tarayya na APC a jihar Adamawa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kotun kolin Najeriya ta kwace zaben Mustapha Usman, dan majalissar APC mai wakiltar Yola ta kudu, Arewa da Gerei na jihar Adamawan Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan da kotun daukaka kara ta baisa Usman nasarar zaben bisa kasancewarshi na biyu a zaben fidda gwani a APC.

Kotun kolin tayi zaman ne bayan da Abdulra’uf Abdulkadir na APC ya daukaka kara zuwa gabanta a korafin mai lamba SC/790/2019.

Kotu ta yanke kwace zaben Mustapha Usman bisa kamashi da yin karyar takardun karatu tare da karyar yin bautar kasa ta NYSC.

Alkalan guda 5 wanda mai shari’a John Okoro ya jagoranta ya bayyana kwace zaben Mustapha Usman tare da umarta INEC da ta bawa wanda yazo na 2 a zaben 2019 na jami’iyyar PDP idan har ya cika dukkanin sharuda doka ta tanada.

Masu Alaƙa  Kano Municipal: APC batada 'dan takarar majalisar tarayya - INEC

DABO FM ta binciko cewa dan takarar kujerar na jami’iyyar PDP Ja’afar Suleiman ne yazo na biyu a zaben da kuri’a 48,476.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020