Home Ra'ayoyi‘Idan Malamai na Allah basu farga ba, shedanun malamai za su cefanar da Musulunci’

‘Idan Malamai na Allah basu farga ba, shedanun malamai za su cefanar da Musulunci’

by Dabo Online
0 comments
Umar Aliyu Fagge

Ra’ayoyi: Idan Malamai na Allah basu farga ba, shedanun malamai za su cefanar da Musulunci, Daga Umar Aliyu Fagge.

Ilimi, tunani da hankali sune matakin farko da mutum yake amfani dashi gurin banbance halak da haram, a kowane matakin rayuwa kuma akan wannan gwadaben ne ake samun masalaha akan wasu sababbin abubuwa da basu taɓa wanzuwa a baya ba, wato ijima’in malamai masu tsoron Allah.

Akwai bukatar daukacin malaman addini sun gane cewa addinin musulunci ba mallakin wata kungiya bane hasalima bai karfafa rarrabuwar kai a tsakanin musulmai ba, don haka ba karamin kuskure bane wata kungiya ko wani mutum yayi amfani da son ran shi gurin fahimtar addinin musulunci kawai domin samun abin duniya.

Dan karamin sani da tunanin da muke da shi ba zai zama hujjar da wasu daidaikun kwadayayun malamai zasu yi amfani da shi ba gurin muzguna mana da tafarkin da muke kai, kwadayayun malamai masu tsoron talauci sun shiga rigar addini gurin kawo shubuha kawai don biyan bukatar wasu mutane daban. Babu wani mahaluki da ya isa ya hana wani malami yin siyasa domin kundin tsarin mulkin Najeriya ya bashi cikakkiyar damar yin hakan, amma kuskure ne babba ace wani malami ya ringa kokarin siyasantar da addinin Allah ta hanyar yin amfani da majalisun karatu ko mambarin juma’a yana tallata wani tare da aibata abokin hammayar sa.

Ba dole sai malamin addini ya yi rayuwar tumasanci da kaskanci ba zai samu ingantacciyar rayuwa, duk mutuncin malami da sanin addinin sa idan har bai guji saka son rai ko shigar da siyasa cikin karatun sa ba, to bashi da maraba da dan asharalle ko Garba Sufa! Addinin Allah na nufin tsantsar gaskiya kuma duk abin da yaci karo da shi ya zama karya abin wofantarwa. Babu wani malamin da zai tsira da mutuncin sa idan har zai bi son rai ko rudin zamani!

Ina magana ne akan danyen hukuncin da wasu daga cikin mutanen da suke ikirarin su malamai ne, nayi imanin cewa kaso ashirin da biyar cikin hamsin daga cikin wadancan malaman ba abin gasgatawa bane hasalima akwai yiwuwar a same su da wata lam’a wacce ta saɓa da koyarwar addinin musulunci, amma wai sune suka ga kyautawar yanke hukunci na hana daukacin mutane sama da miliyan sha biyar aiwatar da sallar juma’a a cikin jam’i.

Wannan hukuncin bai yi kama da na masu hankali da ilimi ba idan muka yi duba na tsanaki akan dalilin da yasa suka yanke wannan hukuncin da kuma damar da Gwamnati take bawa al’umma su fito domin cin kasuwa, domin cunkuso da turmutsutsun da ake yi a kasuwanni mu babu su a masallatan mu!

Sanin kowa ne cewa nau’in kowane mutum tun daga kan kafirai har zuwa marasa addini suna zuwa kasuwa domin cin kasuwanci, saɓanin massalatai inda musulmai ne kadai cikin nutsuwa muke zuwa bautar Ubangijin mu. Amma wannan hujjar ba ta isa wukar kugu ba ga wadancan malaman da su bada shawara a hana bude kasuwa sai massalatai. Allah wadaran naka ya lalace, yanzu anyi yunwa munga kwadayayun malamai masu tsoron talauci ba Allah ba.

Wannan ba sabon abu bane idan mukayi la’akari da yadda ita kanta daular musulunci take tangal-tangal gurin kirkiro sababbin abubuwan da addinin musulunci bai waye su ba, amma ire-iren wadannan malamai sunyi tsit kamar abin da Saudiyya take aikatawa yana daya daga cikin shika-shikan musulunci. Tabbas karshen duniya yazo malaman da ake tsammanin zasu yi hani ga mummuna tare da nuni a aikata alheri wai sune kan gaba gurin ha’intar ubangiji da yaudarar alummar da suka basu amanna shirun duniya akan wadannan lefukan shi yake bata addini a idon wanda ba musulmai ba tare da raina mutanen da ya kamata ace an girmama.

Ya Allah ka tsare mu tare da imanin mu, kada kasa muji tsoron wanda baya jin tsoron ka Ya Allah. 🙏🙏🙏

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00