Tsohon sanatan Kaduna, Kwamared Shehu Sani ya bayyana ‘yan ta’addata ne suka fi addabar jama’a fiye da kwari masu cinye amfanin noma.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta bayyana ta ware naira biliyan 13 domin feshin maganin kwarin gona, DABO FM ta rawaito tsohon sanatan nayin raddi ne akan kudin da aka ware a harkar feshin gona duk da kisan kiyashin dake afkuwa a arewa.
Shehu Sani yace “Ku fara kashe ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, sai mutane su iya zuwa gona domin kashe kwarin gona.”
Ya kara da cewa “Ta yaya zaku kashe kwarin gona kun gaza gamawa da kwari a cikin al’umma.”
Abubuwa dai sun kara tsauri a cikin satikan da suka gabata, inda ‘yan ta’adda ke cin karen su babu babbakar a jihohin arewa musamman Katsina, Borno, Zamfara da sauransu.
https://mobile.twitter.com/ShehuSani/status/1272077581895041024
