Home LabaraiZa a cigaba da rufe wuraren wasannin kwallon kafa – Gwamnatin tarayya

Za a cigaba da rufe wuraren wasannin kwallon kafa – Gwamnatin tarayya

by Dabo Online
0 comments

Gwamnatin tarayya ta ce za a cigaba da rufe dukkanin al’amuran wasanni musamman na kwallon kafa a Najeriya har sai ta bayar da umarnin cigaba.

Shugaban kwamitin yaki da cutar Kwabid-19 na Najeriya, Boss Mustapha ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai akan sabbin tsare-tsare da akeyi na yaki da cutar a Najeriya.

Tin dai a watan Maris, gwamnati ta dakatar da dukkanin harkokin wasanni lamarin da ya sanya aka dakatar da buga gasar Kofin Kwararru na Najeriya ‘NPFL’ sakamakon barkewar cutar ta Kwabid-19.

“Ba na tunanin muna farin ciki da bude wuraren wasanni a fadin Najeriya, musamman kwallon kafa da take tara mutane da yawa.”, cewar Boss Mustapha.

DABO FM ta tattara cewar a ranar Juma’a ne dai gwamnatin jihar Kano ta amince da bude gidajen kallo a fadin jihar.

“Idan sharudanmu sun ce an haramta taro da zai tara mutane sama da 20 in banda a wajen aiki, ba na ganin akwai wani abin birgewa idan aka bari ayi kwallon kafa ko da za ayi babu ‘yan kallo.”

“Kasashen Turai da yawa da suka fara yin wasanni, su suna bin abubuwan a hankali kuma suna tabbatar da kula sosai.”

“Ba mu ji dadin bude harkokin wasannin ba, amma zamu kawo lokacin amma zuwa yanzu, damuwar tana kan abubuwan da aka bude tukun.”

“Za mu cigaba da duba lamarin, mu yi nazari kuma musan abinda za mu yi a gaba.”, inji Boss Mustapha.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00