Labarai

Ina nan da raina ban mutu ba – IBB

Biyo bayan labaran mutuwar tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida da yayi ta yawo a shafiyar yau 15 ga watan Disamba, ta tabbatar labarin babu gaskiya a ciki.

Wasu daga cikin kafafen sadarwa a Facebook ne suka rika yada labaran karyar.

Ibrahim Babangida ta hannun mai magana da yawunshi, Kassim Afegbua, ya karyata labarin.

Ya kuma tabbatar da tsohon Shugaban Kasar yana nan cikin koshin lafiya.

DABO FM ta tattaro daga sanarwar da sanarwar da Kassim ya fitar cewa; “Ina rokon Allah Ya yafewa duk wanda suke so in mutu.”

“Wannan ne karo na 3 cikin wannan shekarar da ake yada irin wannan labarin.”

“Daga karshe, mun godewa duk wadanda suka tuntubemu domin jin gaskiyar lamarin daga ciki da wajen kasa.”

“Ina addu’a Allah Ya kari dukkanmu da lafiya da nisan kwana.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Wallahi zan auri Babangida ko ‘Kwarkwara’ zai yi dani – Budurwa mai son IBB

Dabo Online
UA-131299779-2