Gobara ta cinye wasu ‘yan uwa takwas. Wutar da ta tashi da misalin karfe 5 na yamma ranar Asabar a garin Dan Musa na karamar hukumar Dan Musa, ta yi sanadin mutuwar mutane takwas har lahira bayan sun yi kurmus zuwa baki.
Gobarar ta samo sanadi ne ta dalilin fashewar tukunyar Gas da ake amfani da ita wajen dafa abinci. A cewar bayanai, mutane biyar daga cikin mamatan, matan aure ne, sai kuma uku duk yara ne.
Daga cikin matan auren akwai wata Maryam da ta zo daga Abuja domin ta ziyarci ‘yan uwan na ta. Tun da farkon tashin gobarar, mutane da dama sun yi kokarin balla kyauren shiga gidan don su taimaka, amma kofar ta ki buduwa, har sai da ajalinsu ya yi.
A cewar dan uwan wadanda suka rasun, Mai Iyali, ya bayyana mutuwar a matsayin wacce ta jijjiga su. Kuma za su jima cikin jimamin al’amarin.
Kakakin ‘yan sanda na jihar Katsina SP Gambo ya tabbatar da faruwar wannan iftila’i.
