(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Ina rokon gwamnatin Kano ta kashe ni a bainar jama’a – Wanda ake zargi da kashe yaro

Karatun minti 1

Wani matashi a jihar Kano mai suna Anas Sa’idu dan shekara 22, ya yi kira ga gwamnatin Kano da ta kashe shi ta hanyar rataya a bainar jama’a.

Ana zarginsa dai da sace wani yaro dan shekara 16 mai suna Tijjani mai shekara 16 tare da kashe shi bayan ya rasa inda zai ajiye shi a karamar hukumar Bebeji dake Jihar Kano.

Wanda ake zargin ya bayyana haka ne yayin da rundunar ‘yan sandan Kano ta kama shi ta kuma tusa keyarshi zuwa hako inda ya birne yaron da ya sace.

Da yake zantawa da manema labarai, matashi ya ce; “Ina rokon gwamnatin Kano dan Allah ta kashe ni ko ta rataye ni, wallahi ban taba yin wannan abin ba.”

Yanzu haka ana haka ramin da ya birne yaron domin tonoshi.

A nashi bangaren, kakakin rundunar yan sandan jihar Kano ya ce mahaifin yaron ya kawo korafin sace masa da a ranar 9 ga watan Nuwamba, inda tin daga nan rundunar ta fara bincike, a cewarsa.

“Ya roke mu kan cewa kawai mu rataye shi, aikin dan sanda ba haka yake ba, mun bashi dama ya fadi duk abinda yake so.”

Ya yi kira ga mutane da su kiyaye kan cewa yawanci sace-sace da ake yi, makusanta mutanen ne suka dauke su ko su hada baki da wadanda suka daukesu.

 

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog