Karin aure a wannan lokaci ya zama dole -Dan Isan Zazzau

dakikun karantawa

An yaba da irin kokarin da Majalisar ‘Ina mafita al-umma forum ke yi, wajen daidaita matsalolin ma’aurata tare da sanya albarka ga majalisar.

Mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Malam Ahmad Nuhu Bamalli ne ya yi yabon a lokacin da Majalisar ta shirya babban taronta a Zaria domin lalubo irin matsalolin dake cikin gidajen ma’aurata tare da bada shawarwari don magance matsalolin.

Yabon ya fito ne daga bakin wakilin mai martaba Sarki a taron, Alh. Aminu Sa’idu Zaria Bujimin Arewan Zazzau.

Ya ce, irin aikin da majalisar ke yi abin a yaba ne, na kokarinsu wajen gyara matsalolin ma’aurata, ya kuma yi kira a gare su da su cigaba da irin wannan aikin tare da sanya masu albarka. Inda ya yi alkawari taimaka wa majalisar a duk lokacin da ake bukatar hakan.

Shi kuwa Uban majalisar kuma Dan Isan Zazzau, Alh. Umar Shehu Idris, ya ce; Karin aure ga magidanta ya zama wajibi, duba da la’akari da yawaitar ‘ya’ya mata, hakan zai hana mata da maza fada wa cikin fasikanci.

Ya ce, za su cigaba da taimaka wa majalisar a kowane mataki, don ganin an kara wa mata kwarin gwiwa.

Da yake sanya albarka a wurin taron, Garkuwan ayyukan Zazzau, Engr. Abdulkadir Balarabe Musa, ya nuna jin dadinsa na ganin irin aikin da majalisar ke yi, ciki har da taimaka wa marayu wajen basu ilimi da yin masu sutura.

Ya ce irin wannan aikin ba karamin abu bane ya kuma kamata ta jama’a su maida hankali a kai don samun gafara a wajen  Allah SWT.

Ya kara da cewa suna shirye wajen bada tasu gudummuwar a kowane lokaci don karfafa wa majalisar.

Shugaban taron Mal. Muhamud Abdullahi Barwa, Manaja na Dirv/Alheri Rediyo Zaria, ya ce shekaru hudu kenan wannan majalisa na aikin tukuru, wajen daidaita ma’aurata. Inda ya godewa mahalarta taron tare da yin masu fatan Alheri.

Tun farko, shugaban majalisar, Mal. Bashir Abubakar Magaji Basharata ya bayyana makasudin taron. Ya ce, an shirya ne don gano matsalolin dake addabar ma’aurata tare da bada mafita. Inda ya ce tsawon shekaru majalisar ke gudanar da daidaita ma’aurata inda ya ce akalla sun sulhunta aure fiye da dari uku.

Ya kuma kara da cewa suna ciyar da marayu a lokacin babbar sallah, kuma sukan yi masu sutura a lokacin karamar sallah tare da baiwa iyayen marayu tallafin kudi don kama sana’ a don dogaro da kai.

Ya gode wa mahalarta taron don kara basu goyan baya da hadin kai, inda ya gode wa Dan Isan Zazzau na taimaka masu da yake yi da sauran masu bada gudummuwar su don cigaban majalisar ta Ina Mafita.

Taron dai ya sami halartar wakilin Mai martaba, Hakimai, Alkalai, lauyoyi, da sauran al-umma. Wasu daga cikin mahalarta taro maza da mata, sun nuna jin dadin su na irin amfana da su kayi.

A karshe sun gode wa majalisar Ina mafitan, tare da yin mata addu’a na fatan Alheri, inda su ka ce, za su kasance da ita don samun karuwa.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog