Matashi dan shekara 22 ya kashe matashin da ya sace dan shekara 16 a Kano

Karatun minti 1

Ana zargin wani matashi a jihar Kano mai suna Anas Sa’idu da kashe wani yaro mai shekara 16 da ya sace a karamar hukumar Bebeji ta jihar Kano.

DABO FM ta tattara cewa matashi ya sace dan shekara 16 mai suna Tijjani a ranar 9 ga watan Nuwamba da misalin karfe 5 na yamma a karamar hukumar Bebeji ta jihar Kano.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ya ce sun samu nasarar kama wanda ake zargi bayan mahaifin yaron ya kai korafi wajen ‘yan sanda.

Ya ce an nemi mahaifin Tijjani ya bada Naira miliyan 1.3 da kuma katin MTN na N20,000 a matsayin kudin fansa.

DABO FM ta tattara cewa matashin da ake zargi ya ce ya kashe yaron ne bayan ya rasa inda zai ajiye shi, daga nan ne ya shake shi, kuma birne a wani kauye da ke karamar hukumar ta Bebeji a Kano.

Zuwa yanzu tuni dai aka tono gawar Tijjani a inda Anas ya birne ta.

Da yake yi wa manema labarai jawabi, Anas Sa’idu ya roki gwamnatin Kano da rundunar ‘yan sanda da ta kashe shi ta hanyar rataye domin shima sake shi (Tijjani) ya yi har ya mutu.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog