Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Indiya: Mun samu Dalibanmu cikin koshin Lafiya da kwanciyar hankali – Kwankwaso

2 min read

A makon da muke ciki ne tsohon gwamnan jihar Kano, Engr Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kai ziyara kasar Indiya domin ganawa da daliban da gidauniyar Kwankwasiyya ta tura kasar.

Ranar Asabar, 2 ga watan Nuwambar 2019, Kwankwaso, ya sauka a birnin New Delhi da misalin 8:03 na safe ( 3:33am Najeriya).

Ranar 5 ga wata, Kwankwaso, ya kai ziyarar farko zuwa jami’ar Sharda dake garin Noida a jihar Uttar Pradesh da misalin karfe 2:25pm.

Kwankwaso, ya tattauna da daliban tare da sake yi musu nasiha da nusar da su akan bin doka da oda.

Wakiln DABO FM da ya halarci taron, ya shaida cewa; Kwankwaso ya kuma ja hankalin daliban da su mai da hankali wajen karatu tare da kaucewa dukkanin wadansu ayyukan da zasu bata sunan jihar Kano da Najeriya.

Ya kuma bayyana jin dadinshi kan kan yacce yace ya ga daliban cikin koshin lafiya da farin ciki.

“Alhamdulillah, kamar yadda aka sani, lafiya itace take buya. Mun same ku cikin koshin lafiya, naga dayawa daga cikinku kunyi kyau kunyi haske.”

“Shuwagabanniku da suka taro mu a filin Jirgin sun bayyana cewa sau hudu kuke cin abinci a rana, muna farinciki da haka kwarai da gaske.”

A ziyarar tsohon gwamnan, ya kaiwa daliban da gidauniyar ta tura zuwa jihohin Gujirat da Rajasthan wanda a nan gaba zai garzaya zuwa jihar Maharastra.

DABO FM ta tabbatar da Kwankwaso yana kara duba wadansu makarantu da ake sa ran sake turo wadansu daliban domin yin karatun Digiri na 2.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.