Juma’a: Sallah a masallacin da mutane miliyan 8 suke halarta a kasar Indiya

Ainahin ranar wallafa rahoton: 6 ga watan Yulin 2019, maimaicin Yau.

An gudanar da sallar Idi karamar a kasar Indiya ranar 5 ga watan Yulin 2019.

Wakilan DaboFM sunyi tattaki zuwa garin Agra dake jihar Uttar Pradesh dake kasar Indiya, jihar da take da yawan mutane sama da miliyan 208, wadanda sukafi adadin ‘yan Najeriya gaba daya.

Wakilanmu sun samu halartar Sallar Idi da aka gudanar a masallacin dake cikin ginin Tarihi na Taj Mahal, ginin tarihin da yake cikin gine-gine 7 da suka fi kowanne a duniya. Gwamnatin Indiya ta fitar da kiddiga data ce sama da mutum miliyan 8 ne suka zuwa Taj Mahal a kowacce shekara.

Masu Alaƙa  Azumin Ramadana: Kayan abinci sunyi tashin "Tashin Hankali"
Latsa alamar ”Play” domin kallon bidiyo

An shafe shekaru sama da 21 wajen ginin Taj Mahal, daga shekarar 1632 zuwa shekara 1653. Tanada girman ‘Hectares 17’.

Bidiyo. II

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.