Labarai

Iraniyawa 82, ‘yan Canada 63 da Jamusawa 3 ne suka mutum a hatsarin jirgi a Iran

Ministan kasar Ukraine, Vadym Prystaiko, ya bayyana cewa ‘yan kasar Iran 82, Canada 63, Ukraine 11, Sweden 10, Afghanistan 4 da Ancient Briton 3 ne suka mutum a hatsarin jirgin kasar wanda ya fadi.

Jirgin kasar Ukraine kirar 737 ya fadi a kasar Iran jim kadan bayan tashinshi daga filin tashi da saukar jiragen dake Tehran bayan samun tangardar na’ura.

Gidan Talabijin na birnin Tehran ne ya sanar da haka a yau Larabar 8 ga Janairun 2020.

Raza Jafarzadeh, kakakin hukumar sufurin jirgin saman kasar, ya bayyana cewa mutane 170 ne a cikin jirgin da ya fadi filin tashin da saukar jirage na Imam Khomeini tsakanin biranen Parand da Shahriar.

Jami’in kare hadura a yankin, Pir Hossein Kulivand ya shaidawa manema labarai cewar jirgin, kirar 737 mai lamba 800 ya fara ci da wuta bayan faduwarshi, ya kuma tabbatar da babu wanda yayi rai a cikin fasinjojin dake cikin jirgin su 170.

Karin Labarai

UA-131299779-2