Wani Farfesa dan Amurka, Dakta Craig Considine, mai bin addinin Kiristanci, ya ce Annabin Muhammad SAW, ya nema wa mata ‘yancin su kafin su waye zuwa yanzu da suke gayun iyayi.
Dakta Craig Considine, shahararren marubucin alakar Musulunci da Kiristanci, malami ne a fannin ilimin sanin halayyar dan adam mai karantarwa a Jami’ar William Marsh Rice dake birnin Texas na kasar Amurka.
Ga duk ma’abota shafukan sada zumunta musamman Twitter, masu bin al’amuran da suka shafi addinai, suna cin karo da irin kalaman malamin a kan Annabi Muhammad SAW.
Kasancewarshi mai binciken addini da neman kawo karshen tsangwama da kyara da ake yi wa musulmai musamman a kasar Amurka, a kowanne lokaci yakan fadi irin halayen Annabi Muhammad SAW wanda wasu daga cikin manyan mabiya addinin Kirista kamarshi basa son fada.
DABO FM ta binciko irin kalaman da ya dade yanayi a kan kara fito da halayen ainahi na Annabi Muhammad SAW da nuna abinda yake kira da cewa “Shi masoyin annabi ne.”

Ya ce; “A shekarar 629, Annabi Muhammad zai iya daukar fansa a kan wadanda suka nuna masa tsana, amma bai yi haka ba, ya ce musu ‘God’ Allah mai yafiya ne kuma mai jinkai. Har ma yace musu kowa ya koma gidanshi.” – Dr Craig, Twitter, 8 Jan 2020
Hakan ne yasa ake gayyatarshi zuwa taruka domin tattaunawa a kan addinai tare da yada sakon cewa Musulmai da Kiristoci duk ‘yan uwan juna ne bisa a yacce yace duka Ubangiji daya ake bautawa.
A watan Disambar 2019, Dr Craig ya samu gayyata ta musamman daga Hadaddiyar Daular Larabawa inda ta kai shi ga zuwa babban masallaci nan na Sheikh Zayed Grand dake birnin Abu Dhabi.
Zuwa yanzu malamin ya rubuta litattafai da dama wadanda suka hada da;
- Tattaunawar Wayewa: Mu’amalar Muhammad da Kiristoci.
- Annabin So: Maganar dan darikar Katolika akan Annabi Muhammad
- Musulunci a Amurka.
Da sauransu..
