//
Thursday, April 2

Sojoji sun fatattaki Boko Haram a yunkuri harin Damaturu

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rundunar Sojin Najeriya tace ta samu nasarar dakatar da wani hari da kungiyar Boko Haram tayi yunkurin kai wa a garin Damaturu na jihar Yobe.

Tin da yammacin Lahadi, wasu mazauna yankin suka shaidawa DABO FM jin karar harbe-harbe wanda ta kai ga wasu sun kauracewa yankin.

Kakkakin sashen ‘Operation Lafiya Dole’, Laftanar Chinonso Oteh ne ya tabbatar da fatattakin da jami’an suka yi wa Boko Haram a harin da sukayi yunkurin kaiwa zuwa garin.

Tini dai aka cigaba da gudanar da rayuwa a garin dake kusa da babban titin Gashua a garin Damaturu.

Masu Alaƙa  'Yan Kungiyar Boko Haram sun kwashe makamai dake cibiyar binciken Sojoji a Borno.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020