Labarai

Iyalan Sarkin Saudiyya na zuwa asibitocin Najeriya domin neman magani -Ministan Lafiya

Ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora ya bayyana Najeriya tana karuwa da masu ziyarar bude ido da masu neman lafiya.

Majiyar Dabo FM daga jaridar Punch ta bayyana cewa ministan ya fadi haka ne a babban birnin tarayya dake Abuja ranar Litinin inda yace kasashen duniya daban daban na zuwa Najeriya neman magani shekarun da suka shude.

Ministan yace “Cikin alif dari tara da 50 zuwa da 60 iyalan Sarkin Saudiyya na zuwa Najeriya asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan domin neman magani.”

” Mutane da yawa na zuwa kasashen ketare domin neman magani sabOda yanzu babu anan gida Najeriya, duk kokarin mu da muke yi kenan na dawo da ire iren wadannan injina na duba lafiya yanda zamuyi gogayya da sauran kasashen duniya.”

UA-131299779-2