Labarai

Kwalejin koyar da kiwon lafiya ta Makarfi ta shirya taron wayar da kan Jama’a kan Zazzabin Lassa da COVIC19

A kokarin da ta ke domin taya gwamnatin Jihar Kaduna yaki da cutar Zazzabin Lassa da kuma cutar sarkewar numfashi mai suna COVIC19 da ya shigo wani sashin kasar nan, majalisar dalibai na kwalejin koyar da kiwon lafiya da kimiyya ta makarfi wato Shehu Idris College of Health Tochonology Makarfi, da hadin gwiwar majalisar gudanarwar makarantar, sun shirya taron karawa juna sani da wayar da kai game da alamomin cutar da kuma hanyoyin kariya daga gare shi.
Taron da ya gudana a dakin taro na kwalejin da ke garin Makarfi a Jihar Kaduna, ya samu halartan masu ruwa da tsaki a bangaren kiwon lafiya na kananan hukumomin Makarfi da Sabon gari da shuwagabannin makarantar da malamai da dalibai da kuma sauran jama’ar gari.

Da yake jawabin bude taron, shugaban kwalejin Dakta Sulaiman Usman, ya nuna matukar farin cikin sa ne bisa kokarin da makarantar ta yi wurin shirya irin wannan taro a karo na farko, kuma ya ce, abun damuwa ne matuka ganin yadda cutar zazzabin lassa ke dada yaduwa zuwa wasu sassan kasar nan.

Ya ce, an shirya taron ne domin wayar da kan al’umma domin kuma taimakon kokarin gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed Elrufa’i, saboda yanzu haka gwamnatin ta kudiri aniyar kawar da duk wasu cututtuka da su ke damun al’umma a yau.

Wadannan cututtuka ana samun su ne daga kwayoyin cuta da ke yawo ko’ina, a don haka akwai bukatar jama’a su rika sanin yanda za su yi mu’amala ta yau da kullum, inji Dakta Sulaiman.

Ya kara da cewa, yanzu haka cikin kasashen da wannan cuta ta yi masu illa, Najeriya na cikin wacce take kan gaba a wanda suka kamu da cutar zazzabin lassa.

Ya yabawa gudunmuwar da iyayen kasa musamman hakimin gudumar Makarfi ke bayarwa, domin wayar da kan al’umma a yankunan karkara wanda ya ce hakan zai taimaka wurin bunkasa kiwon lafiya.

Tun farko da yake jawabin maraba, shugaban majalisar daliban makarantar Kwamared Shamsuddin Musa Usman, Ya ce, taron na su, na zuwa ne dai-dai lokacin da gwamnatoci a kowanne mataki suka dukufa wurin fafutikar fadakar da al’umma domin kawar da cututtuka da zummar hana yaduwar shi a sassan kasar nan.

Kuma a matsayin su na kungiya, aikin su ba ya tsaya ne ga bunkasa walwala da jin dadin jama’a ba, hakkin su ne ma su Kula da lafiyar wanda suke jagoranci.

Sannan ya yabawa shugaban kwalejin Dakta Sulaiman Usman bisa cikakken hadin kai da goyon bayan da yake ba kungiyar a dukkanin shirye-shiryen ta.

Ya yi fatan daliban da aka shiryawa taron, su yi amfani da darussan da aka koyar domin bunkasa kiwon lafiyar su.

Shi ma da yake gabatar da kasida a taron mataimakin shugaban kwalejin Mista Istifanus Ishaku ya ce, taron ya zo a kan gaba saboda yanda gwamnati ta dukufa wurin wayar da kan al’ummar ta akan cutar zazzabin lassa da na COVIC19 din.

Ya kara da cewa, cutar lassa ta samo asali ne a kasar Seirra Leone a shekarar 1950, wanda ta yi ta yaduwa a kasashen Afirka har ta shigo Najeriya a shekarar 1969.
Sannan an bayyana bullar shi a wasu jihohin kasar nan ciki kuwa harda Jihar Kaduna.

Kadan daga alamomin cutar sun hada da zazzabi mai zafi da zubar jini ta hanci da ido da tari da jini da kuma canji a garkuwar jiki, inji Mista Istifanus

Sannan ya shawarci al’umma su yi gaggawar zuwa da wanda aka ga alamun ya kamu da cutar zuwa babbar asibiti domin duba lafiyar sa.

A jawaban su daban-daban shuwagabannin kula da bangaren kiwon lafiya a matakin farko na kananan hukumomin Makarfi da Sabon gari, sun bukaci sauran makarantun gaba da sakandare na fadi kasar nan, su yi koyi da kwalejin ta Shehu Idris domin wayar da kan daliban su saboda lalubo hanyar kariya daga cutar zazzabin lassa da na COVIC19.

UA-131299779-2