Labarai

An fara kama matasan Arewa da Hodar Iblis a Indiya

Jaipur, India

A daren ranar Litinin ta makon da ya gabata, yan sandan jihar Rajasthan reshen birnin Jaipur suka cafke wasu yan Najeriya da hodar Iblis mai nauyin ‘gram’ 21 a birnin na Jaipur.

Jami’an sun cafke mutanen guda biyu a wani sumame mai taken “Clean Sweep Operation” da rundunar da gudanar a daren na Litinin bayan da ta dauki watanni tana sanya musu idanu.

DABO FM ta tattara cewar rundunar ta kama Abbas Attahir, mai shekaru 23 dan asalin garin Azare dake jihar Bauchi da Ibrahim wanda ake wa inkiya da Sadauki mai shekaru 28 dan asalin jihar Kano.

Binciken yan sanda yace Ibrahim yaje India a shekarar 2015 domin karantar fannin magani ‘Pharmacy’ wanda ya samu damar kammalawa a 2019. Sai dai tace bayan ya kammala karatun nashi, ya cigaba da zama a kasar ba bisa ka’ida ba.

Haka zalika shima Abbas Attahir, yaje kasar Indiya a shekarar 2016 zuwa wata makaranta a garin Jaipur wanda yayi karatu na tsawon shekara 1 kacal inda daga nan ya bar jihar Rajasthan zuwa jihar Hariyana kafin daga bisani ya dawo Jaipur a shekarar 2019, a cewar yan sandan.

Sai dai rundunar tace tana gudanar da bincike domin ganin ko matashi Abbas Attahir yana da hannu a safarar hodar Iblis da aka kamu su tare da ita.

Rundunar ta kuma tabbatar da cewar wani dan Najeriya ne ya baiwa mutanen biyu Hodar Iblis din ta kuma kaddamar da bincike domin kamo wanda ya basu hodar.

Bayan DABO FM ta tuntubi wasu daga cikin tsofaffin abokan Abbas wandanda suka shafe shekaru 2 tare, sun shaida mana cewar bazasu ce komai akan batun ba sai dai sun tabbatar da cewar “basu kara sanya Abbas a idanunsu a watanni 10 da suka wuce.”

Ko da muka tambayesu dalilin kaurace musu da yayi sun bayyana mana cewar bazasu komai ba.

Haka zalika DABO FM ta tuntubi wasu daga abokan Ibrahim dake birnin Jaipur na jihar Rajasthan, sunki ce wa komai akan batun.

Masu Alaka

Yadda Indiyawan Hindu sukayi wanka da cin kashin Saniya don magance Corona Virus

Dabo Online

Jami’an Najeriya suna hana Likitoci a Indiya baiwa Zakzaky kulawar da ta dace

Dabo Online

An kama dillalin harsashi tare da harsasai 10,000

Dabo Online

Gwamnatin Indiya ta bayar da hutun wasan ‘Jirgin Leda’

Dabo Online

Jirgin zuwa duniyar Wata na Indiya yayi tutsu, sakanni kadan daya rage sauka a kudancin duniya

Dabo Online

Zaben2019: Wasu ‘yan Najeriya mazauna kasar Indiya, sun bayyana murnarsu ga nasarar Buhari

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2