Labarai

Yanzu-Yanzu: Mahaifin matashin da baturiya ta biyo Kano zai kai maganar gaban jami’an tsaro na ‘SSS’

Mahaifin matashin da baturiya ta biyo unguwar Panshekara dake jihar Kano, Malam Isa Sulaiman, yace zai kai maganar gaba jami’an tsaro na farin kaya wato State Security Service.

Matashin ya hadu da masoyiyar tasa ne, Janine Sanchez a dandalin sada zumunta na Instagram a bara inda har magana tayi karfi mahaifiyar matashin ta amince ya auri baturiya Janine Sanchez.

Rahoton Dabo FM ya bayyana cewa mahaifin matashin wanda tsohon dan sanda ne yace ya amince da auren amma fa sai an cika wasu sharuda guda 4!

A safiyar Asabar Malam Isa ya bayyana cewa “Tilas sai hukumomi sun bada umarnin yin hakan ba matsala bane, a matsayi na na tsohon jami’in tsaro ni nasan abinda nake fada, saboda hakan ma ranar litinin zan je naga shugaban jami’an tsaro na farin kaya.”

Sharadi na 2 shine lallai a bar matashin ya karasa karatun sa idan sunje kasar Amurka.

Sharadi na 3 shine Tilas ya zauna cikin addinin musulinci, Malam Isa ya kara da cewa “Duk da ita ma ta amince da hakan, watakil ita ma ta musulinta.”

Na karshe shine dole Baturiya Janine Sanchez ta kawo rubutacciyar yarda daga iyaye ko waliyyinta saboda musulinci bai yarda mace ta aurar da kanta ba.

Nan dai da sati kadan Janine Sanchez zata koma California dake kasar Amurka domin shirye shiryen dowowa bikin ta da masoyinta dan unguwar Panshekara a watan Maris. Kamar yadda KanoFocus ta fitar.

Masu Alaka

Ba’a ga Sarkin Kano Sunusi ko wakilinshi a taron rantsar da Ganduje ba

Dabo Online

Gidauniyar Kwankwasiyya ta kai karin dalibai kasar Dubai da Sudan domin karatun digiri na 2

Muhammad Isma’il Makama

#JusticeForKanoKids: ‘Yan sanda sun sake kubutar da Yaran Kano 2 daga Anambra

Muhammad Isma’il Makama

‘Yan daba sun kai hari, gidan shugaban APC na jihar Kano

Dabo Online

KANO: Zamu kama duk wani dan siyasa, mai kalaman tada hargitsi – Hukumar ‘yan sanda

Dabo Online

Har cikin ma’ajiyar kudade Goggon Birin yabi ya hadiye miliyan 6.8 a jihar Kano

Dabo Online
UA-131299779-2