Mahaifiyar Jaafar Jaafar, mawallafin jaridar Daily Nigerian ta rasu a yau safiyar Lahadi, 22 ga watan Maris 2020.
Da yake bayyanawa a shafukanshi na sada zumunta, Jaafar ya ce za’ayi jana’iza mahaifiyar tashi yau Lahadi a Kwanar Gidan Kankara, Sabon Titi dake birnin Kano kamar yadda addinin Islama ya tanadar.