//
Wednesday, April 1

Gwamnatin tarayya za ta cigaba da yin ayyukan raya kasa da kudin ‘Yan Fansho – Aliero

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Biyo bayan karyewar darajar man fetur a kasuwar duniya, akwai yiwuwar Gwamnatin Tarayya ta cigaba da gudanar da ayyukan raya kasa da kudaden ‘Yan Fansho da suka kai tiriliyan 9.

Shugaban kwamitin ayyuka na Majalissar Dattawan Najeriya, Sanata Muhammad Adamu Aliero ne ya bayyana haka jiya a garin garin Fatakwal yayin wata ziyarar duba aikin titin Fatakwal zuwa Aba, kamar yadda The Guardian ta rawaito.

Sanatan yace; “Akwai bukatar da muka aike gaban kwamitin tattalin arziki kan cewar ayi amfani da wasu daga cikin kudaden ‘yan fansho domin a cigaba da ayyukan raya kasa sa akeyi musamman na tituna. Idan gwamnati ta amince da hakan, za’a aike zuwa majalissa domin ta tabbatar.”

Masu Alaƙa  Gwamnatin Tarayya ta gargadi shuwagabanni akan furta zantuka ‘yadda suka ga dama’

“Idan muka dogara da kasafin kudin shekara, kudaden bazasu ishemu wajen gyaran ayyukan nan ba. Muna bukatar wasu kudaden, ko dai mu nemo su ta wata hanyar gamayya ko kuma muyi amfani da kudaden ‘yan fansho.”

“Daga cikin kudin fanshon, baza muyi amfani da sama da kashi 30 ba. Kudin fanshon ya dade a ajiye, idan mukayi amfani da kashi 30 daga ciki, zamu mayar da kudaden ta hanyar harajin kan hanya. Daga kudaden da zamu samu a kan tituna, zamu mayar musu da kudadensu.”

Karin Labarai

Share.

About Author

•Sublime of Fagge's origin. •PR Specialist •PharmD candidate

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020