Labarai

Jami’an gwamnatoci sun yi wa alkalan kotunan zabe barazana sun saka su yin rashin adalci- Amurka

Kasar Amurka tace tana da shaidu dayawa wadanda suka nuna tsoratarwa da barazana da jami’an tsaro na Soji da DSS sukayi wa mutane da ma’aikatan INEC yayin gudanar da zaben 2019.

Haka zalika kasar ta tabbatar da cewar cewar bincikensu ya bayyana zargin yadda bangaren shari’a bai yi aikin da ya dace ba wajen yin shari’ar zabubbukan ba a dalilin tsoratarwa da alkalai suka fuskanta daga masu madafun iko da sakamakon cin hanci da rashawa.

DABO FM ta tatara cewar binciken na dauke a cikin wani rahoton tsarin kare hakkin dan adama na shekarar 2019 da kasar ta Amurka ta fitar ta hannun ‘Department of State’ a ranar Laraba.

Kasar Amurka tace bangaren shari’ar kasar bai yi aiki a matsayin sashin da yake da mai zaman kanshi wanda yake da iko gudanar da ayyukanshi babu fargaba ko tsangwama.

Haka zalika Amurka tace anyi amfani da jami’an DSS da Sojoji wajen takurawa masu zabe da su kansu ma’aikatan zabe wanda hakan ya haddasa rashin fitowar masu zabe tare da taimakawa wajen siye da siyarwar kuri’ar zabe musamman a zaben zagaye na biyu na jihohin Osun da Kano.

“Misali, kamar tashe-tashen hankula da rigin-gimu da shigar Sojojin cikin al’amuran zabe wanda suke yi har a lokutan kada kuri’a, wanda hakan shi ya kawo matsala a zaben gwamnan Ribas. Rahotanni sun nuna yadda jami’an DSS suka rika yi wa turawan zabe barazana idan suka yi dage wajen kare kayayyakin zabe.

“Jami’an DSS din dai sunyi ta zuwa wajen turawan zaben kafin a fara zabe da lokaci kadan.”

DABO FM ta tattara cewar Amurka tace an samu matsalar cin hanci da rashawa da siyen kuri’u dayawa wanda a 2019 aka fi samun matsalar a jihar Kano, a 2018 kuwa kasar tace matsalar ta auku a jihar Osun dayawa.

“Akwai rahotannin rashawa masu tarin yawa wanda ya hada da siyen kuri’u a zangon lokutan zaben 2018 da kuma 2019. Misalin inda matsalar tafi yawa shine zaben zagaye na biyu na gwamna a jihar Osun (Satumba 2018) da kuma lokacin zaben zagaye na 2 na gwamnan jihar Kano wanda akayi a 9 ga watan Maris 2019.”

Masu Alaka

Rashawar zaben zagaye na 2 na gwamnan Kano tafi ta kowanne a zaben 2019 – Amurka

Dabo Online

Dama can nasan Ganduje ne yaci zaben Kano -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Kotu ta soke zaben dan Majalissar APC a jihar Kano

Dabo Online

Kotu ta kori karar Abba Kabir Yusuf, ta tabbatar da Ganduje

Dangalan Muhammad Aliyu

Dukkanin wakilan jami’iyyu sun aminta da’a soke zabe na 2 da akayi a mazabar Gama – Umar Yakasai

Dabo Online

Kotun ‘Allah-ya-isa’ ta fatattaki Akitu tun ba’a je ko ina ba

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2